‘Yan daba sun farmaki ma’aikacin gidan rediyo a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Wasu ‘yan dabar siyasa sun farmaki wani ma’aikacin gidan Rediyon Premier mai suna Ashiru Umar a lokacin da yake tsaka da aiki a mazaɓar Galadima Primary School cikin ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Rahotanni da dama sun yi nuni da matsalar ta fara ne a lokacin da ‘yan dabar siyasar suka kai masa hari inda suka yi tunanin yana ɗaukar su hoto yayin da suke raba wa masu kaɗa ƙuri’a kuɗi a rumfar zaɓe.

Ashiru Umar Wanda aka yi wa rauni tare da yaga masa kaya, ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da ya masa magani a wani asibiti.

A hannu guda, Ƙungiyar ‘Yan Jarida na ta Ƙasa reshen jiJhar Ƙano ƙarƙashin jagorancin Kwamared Abbas Ibrahim, ta yi Allah wadai da wannan al’amari.

Kwamared Abbas Ibrahim ya ce, ya zama dole NUJ reshen Jihar Kano ta ɗauki matakin karɓa wa Ashiru haƙƙinsa bisa adalci.

Daga nan ya ja hankalin ‘yan jarida da su kasance masu ƙoƙarin kauce wa dukkan inda suke ganin matsala za ta iya faruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *