‘Yan fansho na shirin yin zanga-zanga tsirara kan rashin biyan haƙƙoƙinsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Haɗakar ƙungiyar ƴan fansho ta tarayya a Nijeriya, ta yi barazanar yin zanga-zangar gama-gari a yanayin tsirara, wanda zai gudana a ranar 24 ga watan Nuwamba matuƙar gwamnati ta gaza biyansu bashinsu da ƙarin kuɗaɗe da alawus na tallafi da aka yi musu alƙawari.

Shugaban ƙungiyar, Mukaila Ogunbote ya sanar da haka yayin taron manema labarai jiya Talata a Legas.

Ya bayyana cewa, za su gangamin idan gwamnati ta ƙi biyan su fansho da ƙarin N32,000 da alawus na N25,000 na tallafi da aka amince da shi tun 2023.

Ya ce, ƴan fansho da ke ƙasashen waje za su shiga cikin zanga-zangar a yi da su a duk inda suke a faɗin duniya.

Haka kuma, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ta ya shiga tsakani ta yadda zai umarci Ministan Kuɗi da Akanta Janar na Ƙasa da su saki kuɗaɗe.

A cewarsa, da dama daga cikin ƴan fansho sun rasu sakamakon halin matsin rayuwa, wanda hakan ya sa ba sa iya ɗaukar ɗawainiyar iyalansu.

Kazalika, ya ce yayin da ma’aikata suke karɓar alawus ɗinsu, an bar ƴan fansho cikin jiran tsammani, yana mai suka Ƙungiyar Ƙwadago kan rashin nuna damuwa da lamuransu.

By Babaji