‘Yan fashi sun harbe wani tsohon soja a Abuja

Wasu da ake zargin yan fashi ne, sun harbe wani tsohon soja, Birgediya janar Uwem Harold a cikin gidan sa da ke Abuja.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja cikin wata sanarwa, yace sun tura a fara bincike domin gano wanda sukai wannan aika aika.

Bayan haka, kwamishinan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin da kuma sake jaddada cewa hukumar yan sanda zatai iya bakin kokarin ta domin ganin ta cafko wanda sukai wannan mugun aiki.