‘Yan kasuwa sun daidaita farashinsu na fetur da na matatar Ɗangote

Spread the love

Masu sayar da man fetur masu zaman kansu a ranar Laraba sun daidaita farashin man fetur a Babban Birnin Tarayya don daidaita shi da farashin da suka saya daga Kamfanin matatar Ɗangote.

Bincike ya nuna cewa yawancin gidajen mai sun gyara farashin lita ɗaya na man fetur zuwa Naira 1,200.

Wannan canjin ya biyo bayan cikakken sauƙin tsarin kasuwancin man fetur, wanda ya baiwa Kamfanin Mai na Ƙasa na Najeriya (NNPC) damar kawo ƙarshen yarjejeniyar sayen mai daga matatar Ɗangote.

Wannan ya buɗe ƙofa ga sauran masu sayar da man fetur don su iya siyan mai kai tsaye daga matatar man fetur na Ɗangote.

Ma’anar wannan shi ne, NNPC ba zai ƙara zama shi kaɗai ne mai sayen mai ba, kuma masu sayarwa yanzu za su iya tattaunawa da matatar Ɗangote kai tsaye.

By ukarofi