Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Legas ta ce akwai kimanin mutane miliyan 8.67 mazauna jihar ne ke rayuwa da hawan jini, yayin da ta ke shirin ƙaddamar da shirin gwajin cutar na kyauta a faɗin jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana hakan wa manema labarai a ranar Juma’a a lokacin da ya ke sanar da batun shirin gwajin cutukan hawan jini da na suga da za a yi kyauta a jihar.
Kwamishinan ya ce akwai aƙalla mutane miliyan 3.48 da ke fama da cutar yawan ƙiba da kuma wasu miliyan 1.78 da ke fama da cutar suga.
Ya ce, za a fara aiwatar da shirini gwajin cutukan ne a kyauta daga ranar 28 ga watan Oktoba, zuwa 3 ga watan Nuwamba, 2024.
Farfesan ya kuma ce, shirin wani ɓangare ne da ƙungiyar gwamnonin Nijeriya ke amfani da shi wajen wayar da kan al’umma akan ire-iren cutukan da ke cin jiki ba tare an farga ba, don su kula da kansu yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa, kimanin mutane miliyan 10 ne ake sa ran yi musu gwajin cutukan a Nijeriya, ya na mai kira ga al’umma da su kasance masu zuwa dubiya akai-akai don samun ingantaccen lafiya.