Daga IBRAHIM ABDU ZANGO
Ga duk mai fahimtar yadda abubuwa suke tafiya, za a yi la’akari da abubuwan nan akwai takaici sosai da sosai. Kowacce ƙasa a duniya komi ƙasaitarta a tarihi akwai abubuwan ruɗani a cikinta. Manya-manyan ƙasashen Duniya, wadda ita Nijeriyar tamu ana sakata cikin ƙasashe masu tasowa. Duk da ana yi mata kisisinar gurguntawa, domin kada ta zama zakaran gwajin dafin wannan nahiya ta Afrika.
Gaskiyar lamari, tun lokacin da aka ga tattalin arzikin Nijeriya yana damatsiri wato lokacin Janar Gowon inda ga shi dai yaƙi ake yi. Amma cikin ikon Allah arzikin Nijeriya sai gaba-gaba yake yi domin Naira ko’ina a duniya rurubinta ake yi kamar yanzu ɗin nan da ake mararin Dalar Amurka. Abin da baƙin ciki ainun!
To, kowa ya san ta yadda kuɗinmu na gida mutuncinsa ya zube wanwar. kodayake, masu gidan rana su suke morar faɗuwar Naira, domin suna da damin Dalolin Amurka jingim cikin gidajensu da bankunansu a ƙasashen Turai da Amurka da abin kaico, Dubai!
To malam babu kama suna amma an san ko a lokacin wa’e aka karɓi wata gurguwar dabara wai ita “SAP” ko menene ma’anarta oho? Amma dai ko da turawan Ingila sun ce ba su san wannan kalma ba wai ita “Structural Adjustment Policy”. To don Allah Malam tunda ka ji baturen Ingila ya ce bai san wannan kalma ba, kai ɗan bokon bokoko yaya za ka kinkimo rusa ƙasarka domin samun awalajar Bankin Duniya dana IMF?
Abinda nake ganin ilimin boko bai yi mana rana anan ba koko ‘yan’uwa? Duk duniyar farare da baƙaƙe kowa so yake ya ga ƙasarsa ta yi sama wurin tattalin arzikin ƙasa domin shi ne yake haɓaka rayuwa da zaman lafiyarta. Sannan kuma tashe-tashen hankali yakan kawo rashin natsuwa da kawo firgici na game da zamantakewa. Duk da mutanenmu sun shantake ganin su ba komai ba ne lokaci ne zai kuma fice kamar iskar bazara; Allahu Akbar! komai yanzu ya cuɗe kuma kusan saura ƙiris Allah Ya kiyaye, za a fara gudun hijira, domin yunwa da rashin kwanciyar hankali saboda sharrin masu sharri a ciki da wajen ƙasa.
Ka ga dai yadda abinci yake nema ya gagari talakawa a wannan zamani da muke ciki, kuma sanin gobe sai Allah. Domin gwamnati ta yi ya nata kuma masu ɓatawa suna nasu. Saboda haka, kamata ya yi jama’a su ci gaba da addu’a wacce ita ce kawai mafita duk da wasu masu tsattsauran ra’ayi suna ganin masu cewa a yi addu’ar wawaye ne. To mu dai babu abin yi illa mu roƙi Allah Ta’ala ya ƙara kiyaye wannan ƙasa tamu, domin duk gudun ka sai ka dawo. A nan nake so na ankarar da ‘yan siyasar Nijeriya su san da cewa ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma ko ba jima, ko badaɗe, talakawa za su gane kuma za a gani. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura.
Na ga yawancin ‘yan siyasa ba sa ma tunanin me yake faruwa a cikin da’irar talakawa ba. Sai kawai baje kolinsu, domin cim ma burin siyasa kuma suna bin talakawa da guntun burodi. Wai abin baƙin cikin ma guntun burodin ma wai sai dai su jiƙa shi da ruwa domin suna cikin yunwa! Allah dai ya sauwaƙe wannan badaƙala wacce kullum muke ji cikin rediyoyinmu. kususan na jihar Kano. Akwai sababbin gidajen rediyon da aka kafa domin kamfen ɗin siyasar 2023, kuma su ‘yan siyasa ne masu son ɗanewa kujeru masu daraja a nan gaba amma fa babu ababen da za ka ji illa tsokana da badaƙala, Allah shi tsare, amin. Na san gidan Rediyo Freedom ta yi rawar gani saboda ta hana wani jigon ‘yan taɓargazar siyasa a Kano filin cin mutuncin jama’a sai dai akwai gidajen rediyo biyu su ne ba sa saka wa ‘yan ƙatoɓarar rediyon takunkumi. Saboda, suna samun kuɗaɗen shiga. To akwai lokaci domin NCC hukuma ce wacce ta zuba ido. Nan kaɗan za ta kawo ɗauki. Bissalam.
Kwamred Zango, Kano – Nijeriya, 08175472298
