Ko kun san Zakka ce sirrin arzikin Yahudawa?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Wato Yahuduwa saboda tsangwama da suka yi ta sha tun daga kan fir’auna, ya sa sun sami kalubale a duk inda su ka sami kansu a duniya. Don haka sun kasance Yan cirani a ko’ina. Abu biyu da suka rika sama da komai a koyarwar Attaura shine tauhidin kadaice Allah shi kadai babu sirki a bautarsu. Don haka duk inda su ka zauna zaka ga su na kyamata da kauracewa masu masaukinsu. Abu na biyu shine riko da zakka domin basa wasa da ita, dole ka bada zakka ga community dinka wadda su ke Tarawa Kuma manyan ayyuka da su ke da ita shine samar da jari da guraben karatu ga mutanensu. Idan danka na da hazaka dole ya tafi makaranta mafi kyau a duk inda su ke, ko baka da hali za a biya masa.

Sannan kowane aiki kake sai an tabbatar jarinka ya ishe ka. Kuma ba su cika son yin kananan sana’o’i ba. Tun tali-tali sun gane mahimmancin tattare harkokin kudi ta hanyar bashi don haka su ka mamaye harkokin banki.

Lokacin da aka far musu a kasashen Turai a Karni na 18 sun yi kaura zuwa Amurka. A bakin kogin Hudson, mashigar Amurka a wancan lokacin, sun kafa tebur na karbar bakin Yahuduwa daga Turai…Amma sharadi shine kana zuwa dole ka bada zakkarka kafin ka shiga gari, idan Kuma baka da kudi to kome ka iya shine zakkarka, domin za a haɗa ka da waɗanda zasu koya su kware a hannunka. A Amurka sun kafa makarantu da saka jari a manyan cibiyoyin harkokin kudi da ilimi, yadda a kasa da shekaru Dari suka mamaye kowanne. Tattalin arziki Amurka (da na Duniya) ya zama a hannunsu cikin shekaru 200 da su ka gabata. Shi yasa Kuma baka ganin Bayahude a karamin aiki ko kasashshe, duk inda ka ga Bayahude a kowace kasa zaka samu white-collar job ne da shi. 

Zakka ita ce ginshikin zamantakewar Yahudawa, abinda ya basu edge over all other people a yau. Musulmi ta kasance a cikin shika-shikansu, amma wa ke maganarta? Sannan an hade baki tsakanin malamai da Attajirai wai se shekara za a bayar, Kuma a shekarar ma su wa ke bada ita? Dubi kudin Gulf States, amma dubi Halin da Yemen, Syria, Libya, Palestine ke ciki.

By ukarofi