
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun sojoji na rundunar Birget ta 12 sun yi nasarar halaka sanannen jagoran ƴan bindiga, Kachalla Balla tare da wasu ƴan dabarsa su biyar a yayin atisayen shafe su a Jihar Kogi.
Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Hassan Abdullahi ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar wa manema labarai a ranar Lahadi, a Lokoja.
A ƴan shekarun nan, Jihar Kogi, wadda take da iyaka da jihohi tara ciki har da Abuja, na fama da ƙalubalen ƴan bindiga da garkuwa da mutane da wasu nau’ukan manyan laifuka a sakamakon samun wasu shiyyoyi masu sauƙin tserewa ga masu laifi a sassanta.
Daga ciki akwai yankunan dazuka da ruwa, lamarin da ke ba su damar kafa sansanoninsu ciki sauƙi.
Daraktan yaɗa labaran ya bayyana cewa an yi nasar haka ne a ƙarƙashin Atisayen EGWUA A TITE II a ranar 1 ga watan Satumba, 2025 a ƙoƙarinsu na tsare jihar daga ƙalubalen miyagu.
Ya kuma ce, rundunar da haɗin-gwiwar hukumomin OHF sun yi nasarar katse shirin ƴan bindiga a yankin gadar Agbede zuwa Adanko inda aka halaka wani mutum da ke kai musu kayan aiki.
A yayin haka ne aka ƙwato babur, wayar salula biyu da mazubin alburusan bindigar AK-47.
Ya ƙara da cewa, dakarun Bataliya ta 126 sun yi ba-takashi da ƴan ta’adda a yankin Tunga inda suka halaka ƙarin wasu guda biyu.
