Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Bahaushe na da taken “Gaba Kura, baya Sayaki” anan mu kuma muna iya karawa da sama “Shaho?”
Wannan yanayi kaɗai ya isa mu gane lalacewar siyasa a Najeriya, saboda filin siyasa ya kasance “wane kare ne ba bara ba?”. A ƙasa mai mutane sama da miliyan 220, amma shekaru aru-aru na siyasa a kullum mutanen da aka sani dai su ne ake jujjuyawa.
Idan kuma muka kalli shekaru takwas na Buhari, shi kuma ya zo ya kashe duk wani fata a yanzu ko nan gaba, na samo wani jajirtaccen ɗan Nijeriya wanda za a iya sakawa a gaba domin ceto kasar, saboda babu wani wanda zai iya samun farin jini da amincewa ta talaka irin yadda Buhari ya samu har abada. Kash! sai dai ya ci amanar wannan yarda ta mutane, kuma bai tsaya nan ba sai da ya rushe wannan mahimmiyar amana yadda babu wani sauran tasiri da zata sake yi a fagen siyasar Najeriya nan gaba.
To yanzu cikin wadannan uku, wadanda ake kyautata zaton zasu sami damar tsayawa jam’iyyun APC, ADC da PDP takarar shugaban kasa a 2027, wanene gwanin da zai ceto Najeriya?
Kamun ludayin Tinubu dai ya bayyana karara, yadda ko karkashin Buhari ba a sha wahala haka ba. Bugu da kari, gwamnatin, sakamakon janyewa talakawa tallafin mai, ta karkata ribar da ake samu (a hasashensu na biliyan 500 duk wata), da kudaden shiga da basussuka da take kan ciyowa, kacokan zuwa ga masu mulki a tarayya (Eɗecutive, Legislators da Judiciary) da kuma jihohin 36 da Abuja da kananan hukumomin sama da 700. Hakika idan kaga yadda gwamnatoci ke wadaka da kudaden al’umma ka san cewa hakika wannan gwamnati na makure talaka tana raya mahukunta.
Da alamu dai saboda dosowar zabe, ana bin wasu yan hanyoyi domin talaka ya dauka ana yi da shi ta hanyar bijiro da saukaka abinci da kuma samar da kudade na tallafi/bashi da sauransu ga wasu tsiraru cikin jama’a. Talaka dai an kure shi ta kowacce fuskar haraji, a gwamnatin da ke fatan ta zarce, to idan ta zarce, ya ke nan?
Atiku dai da alamu damarsa ta karshe ce a 2027, kuma idan ADC ta sahale masa tsayawa takarar, shin a yadda ya ke tafiya zai iya kawar da gwamnati mai ci? A nazari na babu wata alama, domin Atiku bai taba shiga zabe da zai iya ci ba irin a 2023, amma da hannunsa ya kayar da kansa. Domin dai a 2019, Obi ne mataimakinsa amma ya bar Obi ya balle daga wajensa ya yi takararsa daban kuma a tsakaninsu su na da kuri’a miliyan 12 a 2023, yayinda Tinubu ya kayar da su da kuri’a miliyan 8 kacal. Sannan saboda ya kewaye kansa da mutane marasa basira ko wadanda ke burin samun biyan wata bukata tasu, ya bari rigimarsa da Wike ta kai har lokacin zabe. Abinda Wike ya nema don bada hadin kai shine, na farko: lallai Iyorchia Ayu ya sauka daga shugaban PDP tunda a tsarin jam’iyyar ba a taba hadawa yanki guda shugaban kasa da shugaban jam’iyya ba. Kemudugus, aka zuga Atiku ya ki yarda da hakan kuma a banza a wofi bayan wata shida kacal da faduwa zabe Iyorchia Ayu yayi murabus. Sannan Wike ya nemi a bashi mataimakin shugaban kasa, kasancewar sa na biyu a zaben fid da gwani, shi ma Atiku ya ki yarda aka dauko wani Gwamnan a yankin Niger Delta aka ba shi, wanda a yanzu shi wannan Gwamna ya koma APC, Atiku kuma na ADC.
A yanzu, da zaben 2027 ke karatowa, Atikun dai ya na maimata kura-kurai irin na baya, domin a yanzu ya na ganin cewa irin su wane da wane idan sun shigo ADC shikenan an ci zabe. Babbar matsalar Atiku a wanna lokaci shine yana abubuwa kamar basaraken gargajiya ba Dan siyasa ba, kuma wallahi a yadda ya dauko, faduwarsa zabe ta karshe ya ke fuskanta. Amma da zai gyara, watakila abubuwa su canza masa a karon karshe.
Ranar da wani tsohon Sanata ke gaya min su na shirin dawo da Jonathan takara saboda Atiku ba zai iya ba kuma ba sa son sa (ya gaya min wata gagarumar hujja mai gamsarwa dalilin da ba zasu bi Atiku ba), na yi nazari sosai na alheri ko akasin hakan. A gaskiya ni ban taba son Jonathan ba kafin ya bar mulki, kuma tun yana mataimakin shugaban kasa nayi rubuce rubuce na sukarsa. Duk da haka, Jonathan ya sami kima mai girma a idona a zaben 2015 sakamakon ceto Najeriya daga tsunduma mummunan yanayi. Akwai mutane da dama, ciki da wajen Najeriya da a dalilin haka su ke girmama Jonathan. Sannan wani tagomashi game da shi shine, kasancewar ya bar mulki tsawon shekaru 12, watakila duk sakarcin da aka yi lokacinsa, yanzu ya goge sosai.
To amma fa kada mu manta akwai abubuwa masu karfi da har abada wasu ba za su so Jonathan ya dawo ba. Misali, yayi amfani da addini sosai wajen raba kan ya Najeriya sannan sakacinsa ya kawo habakar Boko Haram. Ba wanda zai manta tashin bama-bamai a fadin Arewa kuma sakacin gwamnatin sa a wancan lokacin ya fito kuru-kuru. Don haka babu yadda za a yi Jonathan ya sami ƙuri’un Arewa da za su iya ba shi damar cin zaɓe. Daɗin daɗawa, su Wike sun karya PDP ba a Arewa kadai ba har ma a Kudu. A zaben 2023 kuri’a 15,000 kacal ta ci a Kano. Sannan a yanzu ga ADC a fagen siyasar.
To a takaice idan muka yi la’akari da yanayin da ake ciki a yau, wanene cikin ukun nan ya fi damar lashe zaben 2027?
To, kada dai mu manta “Kana taka, Allah na nasa” don haka talakan Najeriya sai in ce ma lamarin fa “SAI ADDUA”
Malam Ali manazarci ne a Kano
