Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ’yan Nijeriya miliyan 25 sun karɓi tallafin kuɗi na ₦25,000 da aka keɓe don rage raɗaɗin talauci. Ministan Kuɗi kuma Mlministan tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai bayan taron majalisar tattalin arziki ta Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta.
Edun ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar matakan tallafa wa ’yan Najeriya don rage wa mutane raɗaɗin da cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati ke haifarwa. A cewarsa, iyalai miliyan biyar ne suka amfana daga wannan shirin kai tsaye na bayar da kuɗi.
Ministan ya kuma ƙara da cewa, a cikin kwanaki biyar da suka gabata, mutane 11,000 sun karɓi tallafin kuɗi na Naira biliyan 3.5 daga shirin bashin tallafin mabuƙata. Wannan ya nuna yadda gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin tallafa wa masu ƙaramin karfi a ƙasar.
Haka kuma, sama da ɗalibai ’yan Najeriya 500,000 ne suka amfana da sama da Naira biliyan 90 da aka bayar a ƙarƙashin tsarin bashin kuɗi na ɗalibai. Wannan shiri ya biyo bayan manufar gwamnatin tarayya na tallafa wa matasa masu karatu a ƙasar don sauƙaƙe musu wahalhalu.
A gefe guda, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mutane 321 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye jihohi da dama a faɗin ƙasar nan. Wannan bayanin ya fito ne a lokacin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce fiye da mutane miliyan 1.2 ne suka rasa matsugunansu yayin wannan ambaliya, tare da lalacewar gidaje fiye da miliyan ɗaya. Bugu da ƙari, gonaki da dama sun salwanta a sakamakon wannan annoba, wanda ya shafi rayuwar dubban al’umma.