’Yan Nijeriya za su fara sayayya da katin Naira a ƙasashe waje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan Nijeriya za su fara sayayya a duk duniya yayin da bankuna a Nijeriya suka sanar da dawo da cinikin ƙasa da ƙasa da katunan naira.

Musamman manyan bankunan Nijeriya uku – United Bank for Africa (UBA), Bankin Wema, da First City Monument Bank (FCMB) ne suka bayyana hakan a wasu saƙonni daban-daban ga abokan hulɗar su.

Bankunan sun tabbatar da sake farfaɗo da hanyoyin biyan kuɗin a cinikayyar ƙasashen waje da katunan su na naira.

Wannan ci gaban dai ya zo ne kimanin shekaru uku bayan da bankuna da dama suka dakatar da hada-hadar kasuwancin ƙasa da ƙasa kan katunan cirar kuɗi na naira.

A sanarwar da UBA ta yi wa kwastomomin kwanan nan, ta ce ci gaba da gudanar da cinikayyar ya yi daidai da ci gaba da jajircewar da ya yi na samarwa abokan hulɗar sa harkokin banki.

“Wannan yana nufin yanzu za ku iya amfani da Katin Nairar ku don biyan kuɗi na yau da kullum, sayayya ta yanar gizo, POS, da kuma ATM a duk faɗin duniya, tare da ƙarin sauƙi da sassauci.

“Idan ba ku yi amfani da katinku kwanan nan ba, yanzu shi ne lokaci mai kyau don sake gano martabar da ke tattare da katin UBA.”

Shi ma da yake sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, bankin Wema ya ce yanzu kwastomomi na iya biyan dala kayan dala da katunan naira.

“Katin ku na Wema Naira zai yi aiki a duk duniya yanzu! Yanzu za ku iya biyan kayan dala akan duk dandamali na duniya da ku ka fi so: Amazon, eBay, AliEɗpress? Netfliɗ, Spotify, YouTube,” inji bankin.

Har ila yau, FCMB, a saƙon da ta aike wa abokan hulɗar sa, ta ce za su iya sayen kayayyaki daga shagunan ƙasa da ƙasa da katin FCMB Verve.

Tsakanin Yuli 2022 zuwa Janairu 2023, yawancin bankuna da hanyoyin hada-hadar kuɗi a Nijeriya sun daina barin kwastomominsu su yi amfani da katunan naira don biyan kuɗin kaya a duniya ta hanyar ATM da POS.

By ukarofi