‘Yan sanda a Kano sun gabatar da mutum 161 da suka kama da aikata laifukan zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Hukumar ‘yan sanda a Jihar Kano ta cafke mutum 161 kan laifin ƙwacen akwatin zaɓe da sauran laifuka da suka danganci zaɓen.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Muhammad Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da waɗanda aka kaman ga manema labarai ranar Lahadi a Kano.

Ya ce sun kama waɗanda lamarin ya shafa ne yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi ranar Asabar a jihar.

Ya ce baya ga satar akwatin zaɓe, an kama wasunsu bisa zargin sayen ƙuri’a da kuma yunƙurin cinna wa ofishin INEC wuta a jihar.

Ya ƙara da cewa, an ƙwace makamai daban-daban daga hannunsu.

“Mun kama mutum 161 yayin zaɓe. An yi kamen ne kan aikata laifukan ƙwace akwatin zaɓe da sayen ƙuri’u da kuma yunƙurin ƙona ofishin INEC,” in ji Kwamishinan.