
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda a Jihar Katsina sun yi nasarar kuɓutar da mutum 361 daga hannun yan ta’adda a shekarar 2024.
Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da hakan a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin nasarorin da rundunar ta samu acikin shekarar.
Ya ce mutanen tuni aka miƙa su ga iyalan su yayin da suka kashe ƴan bindiga 40 a wurare daban-daban a faɗin jihar.
“Mun kuma samu nasarar kama ɓarayin shanu guda 81 da gano shanu da suka sata guda 2081.”
Har’ilayau, jami’an ƴan sandan sun kama yan fashi da makami guda 196 da kuma mutum 100 da laifin aikata fyaɗe.
ASP Sadiq ya kuma sanar da kama mutum 23 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Duk dai a shekarar da ta wuce ƴan sandan sun sun kama mutane 573 da aikata laifuka daban-daban, kamar yadda jami’in ya bayyana.
Ya ce a yayin da ƴan sanda ke gudanar da binciken waɗanda aka kama, an gano bindiga ƙirar AK47 guda 7 da ƙirar gida guda 3 tare da harsasai masu yawa.
Ƴan sandan sun kuma samu ƴan bindigar ɗauke da kakin soja da na ƴan sanda a cewarsa.
ASP Abubakar Sadiq ya kuma miƙa godiya ga hukumar a jihar da al’umma da kuma manema labarai bisa ƙwazo da hazaƙa da goyon baya da suka ba su.
