
Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanonin waya na Telecoms sun miƙa takardar buƙatar ƙara farashi ga Gwamnatin Tarayya da kaso 100.
An miƙa kundin ne ga Hukumar Sadarwa ta NCC don warware matsalolin tashin farashin gudanarwa da hauhawar farashi da ƙarin adadin kashe-kashe.
Shugaban Kamfanin MTN a Nijeriya, Karl Toriola ya faɗi hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, inda ya ce babu tabbas kan cewa ko NCC za ta amince da buƙatar.
Ya ce yana da muhimmanci su ƙara farashin kasancewar kamfanonin suna fuskantar matsalolin hauhawar farashin gudanarwa yayin ayyukansu.
Ya kuma ce duk da cewa hakan na tattare da ƙalubale, yana kyautata zato ga masu gudanarwa kan yanke hukuncin da ya dace.
Ganin yadda Nijeriya ke fuskantar matsalolin hauhawar farashin kayayyaki ne ya sanya ƙungiyoyin ALTON da na kamfanonin waya suka yi kira ga gwamnati da ta shirya tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki don neman mafita game da al’amarin, kamar yadda suka bayyana a wata sanarwar haɗaka.
