
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an ƴan sanda a Borno sun gano wasu makamai masu linzami guda uku da kuma dakatar da fashewar bom a jihar.
Kakakin ƴan sandan, Nahum Daso ya ce an gano makaman ne a yankin Dala Kafanti na Maiduguri, babban birnin jihar a ranar 2 ga watan Janairu, 2025.
A ranar Alhamis ne wata mai suna Asabe James ta ruwaito wa hukumar ƴan sanda cewa ta ga wani buhu dake ɗauke da wasu ababen zargi a bayan gidanta inda rundunar ta aika da jami’an kula da ababan fashewa (EOD) zuwa yankin.
Daga nan ne jami’an suka garzaya yankin tare da umartar al’umma da su nesanta kawunansu daga wajen inda a lokacin ne suka gudanar da bincike tare da gano makaman.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Yusufu Mohammed Lawal ya tabbatar wa al’umma cewa za su cigaba da jajircewa wajen ganin an samu tsaro da zaman lafiya a yankin, ya na mai kira da su ba su haɗin kai wajen aiko da rahoton duk wani abin zargi ta lambobi kamar haka; 08068075581/08023473293
