‘Yan sanda sun cafke ‘yan fashin intanet a Keffi

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘yan sanda a garin Keffi, jihar Nasarawa, ta cafke wasu matasa su shida masu fashi a intanet da aka fi sani da ‘Yahoo Boys’.

Sanarwar manema labarai da rundunar ta fitar wadda ta sami sa hannun mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, a madadin Kwamishin ‘Yan Sandan Jihar, ta nuna biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu game da harkokin ɓatagarin ne sai jami’anta suka yi musu dirar mikiya a maɓuyarsu da ke G.R.A Keffi inda aka kamo su.

DSP Ibrahim Muhammed Siraj shi ne jami’in da ya jagoranci dakarun da suka samame a maɓuyar ‘yan fashin a ranar 6 ga Agustan da muke ciki.

Matasan da lamarin ya shafa su ne: Vincent Damisa, ɗan shekara 23, Monday Desmond, ɗan shekara 18, Donald Godwin ɗan shekara 20, dukkansu ‘yan asalin jihar Edo.

Sai kuma Henry Chukwuemeka, ɗan shekra 18 daga Imo da Emmanuel Ibiala, ɗan shekara 27 daga Cross river da kuma Dakuruk Abel, ɗan shekara 28 daga jihar Filato.

Abubuwan da aka gano a wajen matasan, sun haɗa da kwamfuta samfurin ‘Laptop’ guda 22 da sauransu. Tuni aka kwashi matasan zuwa Lafia babban birnin jihar don zurfafa bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, AIG Bola Longe ya yaba da wannan nasarar da jami’an rundunar suka samu, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan ci gaba da gudanar da aiki bisa ƙwarewa.