Gobe ne farkon sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi

Sakamakon rashin samun labarin ganin wata a faɗin Nijeriya daga Kwamitin Neman Wata na Ƙasa ja jiya Lahadi wanda shi ne 29 ga Zul-Hajji 1442, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana gobe Talata a matsayin farkon sabuwar shekarar Musulunci, wato 1 ga Muharram, 1443AH.

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama (NSCIA), ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar manema labarai ta hannun Kwamiti Mai Bai wa Sarkin Shawara Kan Harkokin Addini wadda sakatarensa, Farfesa Sambo Wali Junaidu (Wazirin Sokoto) ya sanya wa hannu.

Da wannan, Sarkin ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi na ƙasa baki ɗaya murnar sabuwar shekarar, tare da addu’ar samun shiriya da rahmar Allah.

Daga nan, ya yi kira ga al’ummar Musulmi na ƙasa da a ci gaba da yi wa Nijeriya fatan samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *