Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda sun daƙile yunƙurin hare haren ‘yan bindiga da satar mutane a ƙauyen Fulalawa da ke ƙaramar hukumar Musawa a Jihar Katsina.
A wata sanarwa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu,ya ce bayan samun bayanan sirri cewar ‘yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun Kai hari har da satar mutane a ƙauyen Fulalawa,nan take ‘yan sanda da taimakon jami’an tsaro na CWC suka fara ɓarin wuta da ya tilastawa ‘yan bindigan ja da baya,wasu a cikin su ana zargi sun gudu suna ɗauke da manyan raunuka.
Kafin jami’an tsaron su shiga ƙauyen, ‘yan bindigan sun farfasa shaguna da sace mutane da dama kafin zuwan jami’an tsaro a ƙauyen a cewar sanarwara.
Jami’an tsaro sun sami ceto mutanen da aka ɗauka da babura guda biyu wanda ‘yan bindigan ke amfani da su wajan aikata ta’addanci.
DSP Abubakar Sadiq ya ce jami’an tsaron za su cigaba da ƙoƙarin kamo ‘yan bindigan da suka tsere.
Kwamishinan ‘yan sanda a Katsina CP Ali Umar Fage ya yaba wa jami’an sa bisa nuna ƙwarewa da suka nuna wajan daƙile harin.
Ya tabbatar wa al’ummar Jihar Katsina cewar ‘yan sanda a shirye suke a ko da yaushe sa tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma.
