

Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne wani Mista Ugochukwu Onuorah mai shekaru 30 da ƴan dabarsa suka musanta batun karɓar miliyan N100 daga marigayi ɗan majalisar Anambara, Hon. Justice Azuka, kamar yadda wani rahoto daga kafafen sada zumunta ya bayyana, a madadin haka ya ce ɗan majalisar ya ƙi biyan su miliyan N20 ne da suka buƙata daga gurinsa.
A ranar 24 ga watan Disambar 2024 ne aka yi garkuwa da Azuka, wanda shi ne ɗan majalisar jiha da ke wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa ta 1, akan hanyarsa ta zuwa gida don hutun bukukuwan ƙarshen shekara.
Daga bisani a ranar 6 ga watan Fabrairu ne jami’an tsaro na haɗaka suka gano gawarsa bayan gudanar da wani atisaye.
A lokacin da aka gurfanar da Onuorah da mutanensa a babban ofishin ƴan sanda na jihar, ya bayyana cewa ba harbe ɗan majalisar suka yi ba, saidai an masa dukan da ya sa ya fita daga hayyacinsa.
Amma wannan batu na Onuorah akwai cin karo da na ƴan dabar tasa inda suka ce kasancewar Azuka bai biya N20m da suka cimma matsaya a kai ba, hakan ya sa Onuorah ya bindige shi har lahira a ranar 24 ko 25 na watan Disamba.
A lokacin da ya ke magana, Kwamishinan ƴan sandan, Nnaghe Obono Itam yayin gurfanar da su da makaman da aka ƙwato a hannunsu, ya ce za a cigaba da bincike game da lamarin tare da ɗaukar matakin doka akan duk wanda samu da hannu a cikin laifin.
