‘Yan sanda sun kama mai safarar yara mata zuwa ƙasar Mauritania

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda da ke aiki a rukuni na 2 na yankin Onikan a Jihar Legas, sun yi nasarar kama wata ƴar safarar ƴan mata daga Nijeriya zuwa ƙasar Mauritania domin yin ayyukan da suka shafi karuwanci.

Kakakin rundunar, CSP Umma Ayuba ta bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Laraba, inda ta ce a ranar 22 ga watan Maris ne aka kama mai laifin a jihar.

Ta ce, jami’an Leƙen Asiri na ZIRS ne suka gudanar da atisayen kamen, inda suka cafko mutane biyu da ake zargi da hannu a laifin, waɗanda tuni suka amsa aikata laifin da ake tuhumar su da a kai.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ta ce, wata mata ce da ke gidan yari sakamakon irin aikin ta haɗa ta da wata ƴar Mauritania, wadda ta nemi da ta riƙa samo ƴan mata ƴan ƙasa da shekaru 22 da za riƙa amfani da su wajen karuwanci ana biyanta.

Ta kuma ce, ana ba ta N50,000 ga kowacce yarinya ta yi wa hanyar zuwa Mauritania.

Bugu da ƙari, ta ce daga cikin ƴan matan da ta tura, akwai ƴarta mai shekaru 19. Haka kuma, ta karɓi aƙalla kimanin Naira 500,000 daga dillaliyar ta Mauritaniar daga sadda ta fara aikin.

Ita kuwa ta biyun, cewa ta yi ta farkon ne ta ba ta aikin samo ƴan mata da nufin sama masu ayyukan gida a Mauritania.

By Babaji