
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya tafi Dakar, Babban Birnin Senegal domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai a ƙasar.
A ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara ne ake gudanar da bikin samun ƴancin kan, wanda ya kawo ƙarshen mulki jagororin Faransa a shekarar 1960, inda ake gudanar da harkokin da suka shafi fareti da wasu taruka na gargajiya.
Hakan ya biyo bayan gayyata ta musamman da Shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye ya yi wa Shugaba Tinubu sakamakon alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Za a gudanar da taron ne a filin taro na Place De La, inda Shugaba Faye zai karɓi baƙoncin Shettima da wasu manyan ƙasashe daban-daban na Afirka da kuma daga wasu Nahiyoyi.
Ana tsammanin Mataimakin shugaban ƙasar ya dawo Nijeriya a gobe, bayan kammala taron na kwana ɗaya, kamar yadda mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na Shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda.

