Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Dikko Raɗɗa ne ya faɗi haka a lokacin da shugabannin ma’aikatun gwamnatin jihar ƙarƙashin babban jojin jihar Mai Shari’a Musa Ɗanladi suka kai masa ziyarar gaisuwar barka da sallah a fadar gwamnatin jihar.
Ya ce yakamata su zage damtse wajen ganin sun aiwatar da ayyukan kasafin kuɗin wannan shekara saboda lokaci na tafiya.
Gaisuwar ta haɗa da ta’aziyar mahaifiyar gwamnan wanda alƙalai da kungiyoyi masu zaman kansu suka halarta.
Da yake jawabi shugaban tawagar Mai Shari’a Musa Ɗanladi Abubakar ya shaidawa gwamnan cewa sun zo suyi masa barka da sallah kamar yadda suka saba a duk shekara bayan kammala azumi da kuma yi masa ta’aziyar rasuwar mahaifiyar sa.
Daga nan sai babban jojin ya tunatar da shugabannin hukumomi da su sani duk abin da suka aiwatar Allah na ganin su”in kunyi daidai Allah ya sani”inji mai shari’a.
Ya bayyana cewa” dukkanin mu munyi rantsuwar kama aiki,kuma mun san girman rantsuwa”saboda haka ya kira ga ma’aikatan jihar da su sa gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da ayyukan su.
Babban jojin ya kuma jajanta da jimamin babban rashi da gwamnan yayi na mahaifiyar sa.
Gwamna Dikko Raɗɗa yayi godiya da irin wannan ziyarar tare da kira da waɗanda ke wurin da su ɗau darasi kan maganganun da mai Shari’a yayi waɗanda suke ɗauke da wa’azi tare da jan hankali.
Tawagar ta ƙunshi sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari da shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Falalu Bawale da manyan sakatarorin gwamnati
