‘Yan sanda sun kama sojan bogi da ke fashi da makami a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sanda da ke sintiri sun kama wani mutum mai suna Andy Edwards mai shekaru 39 da yake iƙirarin shi soja ne da ke yi wa mutane fashi da makami a Legas.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama sojan a ranar Lahadi.

SP Hundeyin ya bayyana cewa sojan bogin mai iƙirarin shi Kaftin ne, yana bayyana kansa a matsayin mai sayar da kayan ƙawa, inda yake kiran mutane da, sunan zai ɗauke su aiki, sai ya yi masu fashi da makami, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce asirinsa ya tonu ne bayan ya yaudari wata yarinya a matsayin zai ɗauke ta aiki, daga bisani ya yi mata fashin motarta da wasu muhimman kayayyaki.

SP Hundeyin ya qara da cewa kama sojan bogin ya biyo bayan binciken da suka gudanar bayan ƙorafin da ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa ta kai masu a kan sace mata mota ƙirar Lexus mai lamba RX330 SUV.

“A binciken da muka gudanar a gidan wanda ake zargin ya kai mu ga gano mota ƙirar Ford Edge SUV mai lambar injin KRD 276 EG da keken ɗinki da mashin ɗin cire kuɗi da layin waya guda shida.

“Haka nan kuma mun gano na’u biyu na kayan soja da kuma lambar mota AFL 469 GD.

“A daidai lokacin da ake kammala bincike, mai motar ƙirar Ford SUV ta zo ta amsa, yayin da ake shirin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu,” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa a shirye suke wajen katse hanzarin duk wani marar gaskiya a Jihar Legas, ta hanyar kamawa da kuma gurfanar da su a gaban kotu.