ASUU ta ƙara tsawaita yajin aikin da take yi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i a Nijeriya, ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take gudanarwa da ƙarin watanni 6.

Jaridar Punch ta rawaito cewa matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi a ranar Litinin game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati.

An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja, babban birnin Nijeriya.

Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni tana gudanar da yajin aikin da ya tilasta wa ɗaliban jami’o’in gwamnati zama a gida.

ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne hanyar samun mafita ga tarin buƙatun da ta gabatar wa gwamnatin Nijeriya ciki har da batun inganta musu albashi.