Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da cafke Naomi Silekunola, tsohuwar matar Ooni na Ile-Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Hakan ya biyo bayan wani mummunan turmutsitsin da ya faru ne a wajen bikin yara da ta shirya wanda ya faru a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba, 2024, a babbar makarantar Islamiyya, Bashorun, Ibadan, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar ƙananan yara da dama, tare da jikkata wasu.
A wata sanarwa a ranar Alhamis, Osifeso Adewale, kakakin rundunar ‘yan sandan Oyo, ya ce yara 35 ne suka mutu yayin da wasu 6 suka samu raunuka daban-daban a sakamakon lamarin.
A cewarsa, “an kama mutane takwas da hannu a cikin lamarin.”
“Daga cikin waɗanda aka tsare akwai Silekunola mai shekaru 31 da Fasasi Abdulahi mai shekaru 56 shugaban makarantar.
“Sauran mutanen da aka kama sun haɗa da Genesis Christopher, Tanimowo Moruf, Anisolaja Olabode, Idowu Ibrahim, da Abiola Oluwatimilehin, masu shekaru tsakanin 25 zuwa 52.”
Rikicin dai ya haifar da bincike, inda aka mayar da shi sashin kisan kai na sashen binciken manyan laifuka na jihar.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ne ya jagoranci binciken.
Osifeso ya tabbatar wa jama’a cewa “za a yi adalci a kan haka” ya kuma jaddada cewa za a ƙara yawan sintiri na ‘yan sanda a yankin domin tabbatar da tsaro da kuma daƙile tashe-tashen hankula.
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta jajanta wa iyalan da wannan iftila’i ya shafa tare da ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da bayar da lambobin tuntubar jama’a na gaggawar.
Tun da farko dai gwamnatin jihar Oyo ta sanar da cewa an tsare waɗanda suka shirya taron.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da gwamna Seyi Makinde ya fitar, inda ya ba da tabbacin gwamnati za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace dangane da lamarin.
Sarauniya Naomi ta saba shirya irin waɗannan bukukuwan kowace shekara wata ƙungiya mai zaman kanta, Wings Foundation, musamman a Akure, inda take zaune. Sai dai wannan taron na musamman wanda ya rikiɗe zuwa ruɗani, an yi shi ne a Ibadan.
Rahotanni sun nuna cewa cunkoson da aka yi a makarantar Islamiyya ta Bashorun ya haifar da turmutsutsu, inda wasu mutane suka suma saboda tsananin zafi.
A halin da ake ciki, fadar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ta jajanta wa iyalan yaran da suka rasa rayukansu a wajen bikin al’adar da aka yi a Ibadan.
Kakakin Ooni ya bayyana juyayin gwamnatin jihar Oyo da kuma iyalan yaran da suka rasa rayukansu a wannan ibtila’in.
Fadar ta kuma nuna goyon bayanta ga tsohuwar sarauniyar, inda ta ce ta na kula da yara da kuma shirya irin wannan taron a jihar Osun lokacin da take sarauniya.
Mai magana da yawun fadar ya ce, “A lokacin da take a gidan Oodua a nan sarauniya, Miss Naomi Silekuola Ogunseyi ta nuna ƙauna da kulawa ga ‘ya’yan Ile-Ife ta hanyar irin waɗannan abubuwan da ta aiwatar da su cikin sha’awa domin tallafa wa ‘ya’yan iyaye marasa galihu a duk watan Disamba.
“Majalisar Oduduwa ta yi alƙawarin tallafa wa duk wani ƙoƙari da aka yi na kawo ta’aziya da waraka ga waɗanda wannan babban rashi ya shafa.
“Majalisar Oduduwa ta yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don hana faruwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba, tana mai jaddada buƙatar bin ƙa’idojin tsaro da tsare-tsaren kula da yara a cibiyoyin ilimi.
“Yayin da lamarin ya buƙaci a yi tunani mai zurfi da alhakin gamayya, za mu so mu nuna rashin jin daɗinmu game da halin rashin ɗa’a na wasu masu rubutun a yanar gizo waɗanda suka zaɓi su ba da mamaki a wannan mummunan lamari maimakon kare mutuncin aikin jarida.
“Majalisar ta Oduduwa tana ƙarfafa dukkan masu ruwa da tsaki tun daga jami’an gwamnati har zuwa kafafen yaɗa labarai da ’yan ƙasa da su haɗa kai wajen tausayawa da tattaunawa mai ma’ana. Mu girmama abubuwan tunawa da marigayin ta hanyar kulawa, girmamawa, da riƙon amana a cikin al’ummominmu,” inji sanarwar.
