‘Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kisan wata mata da aka yi wa cunen satar yara a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kaduna ta yi tir da kisan wata mata da aka zarga da satar yara a yankin Maraban Jos da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta jihar, inda ta bayyana haka a matsayin rashin imani kuma barazana ga hukuncin doka.

Ta ce, an halaka matar ne a ranar Asabar a lokacin da wasu ɓata-gari suka zaƙulo ta daga ofishin ‘yan sanda, sannan suka banka mata wuta duka da yunƙurin bata kariya daga jami’an tsaro.

A sanarwar da rundunar ta fitar ta Kakakinta, DSP Mansir Hassan, ta ce ofishinta da ke Maraban Jos ya samu rahoton kai wa matar farmaki da misalin ƙarfe 10 na safe bisa zargin wanda babu wani abin da ke goyon bayansa.

Akan haka ne DPOn yankin ya tura jami’an tsaro domin ceto matar tare da kai ta ofishin ‘yan sandan domin bata kariya da kuma gudanar da bincike akan zargin.

Saidai duk da wannan mataki, daga bisani ɗaruruwan fusatattun matasa sun kutsa cikin ofishin tare da ciro ta daga ofishin, inda a lokacin ne suka cinna mata wuta.

Rundunar ta ƙara da cewa, marigayiyar ‘yan asalin Maraban Jos ce, tana mai cewa babu wani ko wasu da ke da ikon ɗaukar doka a hannunsu.

Kazalika, sanarwar ta ce an kama mutane da dama da ake zargi da hannu a aikata ɗanyen aikin yayin da kuma ake cigaba da farautar sauran.

By Babaji