Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan sanda sun kama wani matashi mai suna Aliyu Sani ɗan shekara 19 da haihuwa da yin sojan gona da ƙoƙarin amfani da bindigar katako ya aikata fashi da makami.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sanda a Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace wanda ake zargi yabi wani mutun dake tafiya a ƙasa yana biye da shi da bindiga a hannu yana ƙoƙarin yiwa matafiyin fashi.
A cewar DSP Abubakar Sadiq bayan da yan sanda suka sami bayani na yunƙurin fashin, nan take suka garzaya unguwar ƙofar sauri cikin garin Katsina a wurin da ake yunƙurin fashin, ‘yan sanda sun sami nasarar kama wanda ake zargi.
Bincike na farko da ‘yan sandan suka gudanar,sun gano bindigar da wanda ake zargi ya yi amfani da shi,bindigar matako ne, DSP Abubakar ya ce.
Kwamishinan ‘yan sanda a Katsina CP Ali Umar Fage ya jinjinawa jami’an tsaro da aaal’ummar ƙofar Sauri bisa turjiya da suka nuna har sai da Yan sanda suka kama wanda ake zargi.
