‘Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashewar bututun mai a Ribas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, ta ce ta kama mutum biyu domin yi musu tambayoyi dangane da fashewar bututun mai na Trans-Niger a Bodo, ƙaramar hukumar Gokana ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ta shaida wa manema labarai a Fatakwal a ranar Talata cewa, an yi hakan ne domin tabbatar da ko lamarin ya shafi zagon ƙasa.

Iringe-Koko ya bayyana cewa, lamarin da ya faru da tsakar daren ranar Litinin, ya lalata bututun mai na Shell (SPDC) da ke jigilar ɗanyen mai zuwa tashar Bonny Termin’l, wani muhimmin cibiyar fitar da ɗanyen mai.

A cewarta, jami’an tsaro ne suka gano fashewar bam ɗin a lokacin da suke sintiri na yau da kullum a yankin.

“Masu gudanar da ayyukan sun lura da lamarin kuma nan da nan suka sanar da hukumar ta SPDC cikin sauri ta ɓullo da ƙa’idojin aminci da suka dace, gami da rufe bututun da abin ya shafa.

“Yanzu an shawo kan lamarin, kuma babu wata barazana ga mazauna ko muhalli,” inji ta.

Iringe-Koko ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar da kuma tantance irin ɓarnar da aka yi.

Iringe-Koko ya ce “Rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an gano waɗanda ke da alhakin wannan laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.”

Kakakin ‘yan sandan ya buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu da taka-tsan-tsan, yana mai cewa, “Hukumar ta himmatu wajen kare lafiyar jama’a.”

Ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su kai rahoton duk wata matsala ta tsaro ta lambobin gaggawar ‘yan sanda: 08032003514 da 08098880134.

Fashewar ta faru ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara taɓarɓarewa sakamakon shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa Ngozi Odu.

Idan kuma za a iya tunawa, a baya-bayan nan ne wasu ƙungiyoyin tsagerun suka yi barazanar kai hari kan bututun mai a yankin Neja-Delta a matsayin martani ga hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na hana raba kuɗaɗen shiga ga Ribas.

By ukarofi