Ma’aikatan Jihar Kano za su samu albashin watan Maris kafin Sallah – Sakataren Gwamnati 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa da ma’aikatan gwamnati cewa za a biya su albashinsu kafin bikin ƙaramar Sallah, wanda ake sa ran fara biya daga ranar 25 ga Maris.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Faruk Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin.

Jaridar Manhaja ta rawaito cewa an shirya taron manema labarai domin sanar da al’umma kokarin da gwamnati ke yi don kauce wa matsalolin da aka fuskanta wajen biyan albashin watan Fabrairu.

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Malam Ibrahim ya ce gwamnati tana sane da kusantowar bikin Sallah, kuma za ta tabbatar da biyan albashin watan Maris kafin lokacin.

A cewarsa, dole ne a tantance ma’aikatan gwamnati a jihar kafin a biya su albashi na watan Maris domin kauce wa duk wata matsala da aka fuskanta a baya.

Malam Ibrahim ya ce wannan mataki ya zama dole ne sakamakon korafin ma’aikata kan matsalolin da suka hadar da cire wasu kudade daga albashinsu na watan Janairu da Fabrairu.

By ukarofi