Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan sandan Birtaniya sun kaddamar da farautar wani fursuna haifaffen Najeriya, Temitope Segun, wanda ya tsere daga tsarewa yayin da ake kai shi daga kotu a yankin kudu maso gabashin London.
Rahotanni sun nuna cewa Segun mai shekaru 25 yana zaman hukunci ne saboda laifin safarar miyagun ƙwayoyi masu tsanani (Class A drugs) kafin ya tsere a ranar Litinin, 8 ga Yuni, 2026.
A cewar Rundunar ’Yan Sandan Metropolitan, an ga Segun na ƙarshe a kusa da Woolwich High Street da misalin ƙarfe 6:40 na yamma agogon Birtaniya (BST) bayan zargin da ake masa na kai wa wani jami’in tsaro hari yayin da ake kai shi daga Kotun Bromley Magistrates’ Court zuwa Gidan Yarin Thameside (HMP Thameside).
An ce ya yi nasarar rinjayar wani jami’in tsaro a cikin motar da ke ɗaukar fursunoni, wadda kamfanin Serco ke gudanarwa, kafin ya tsere daga wurin.
Kamfanin Serco ya tabbatar da cewa shi ne ke kula da jigilar fursunonin, tare da bayyana cewa ana gudanar da bincike kan lamarin.
“An samu wani lamari a yammacin ranar Litinin, 8 ga Yuni, a Woolwich. Ana gudanar da bincike kan lamarin,” inji kakakin kamfanin Serco.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa wani jami’insa ya samu raunuka a yayin faruwar lamarin kuma a halin yanzu yana jinya a gida.
Bincike ya nuna cewa lokacin da ya tsere, Segun na sanye da baƙar jaket, baƙaƙen wando da kuma baƙaƙen takalma. Haka kuma an bayyana cewa yana da alaƙa da yankunan Plumstead, Abbey Wood da Woolwich.
Jami’ar bincike ta Rundunar ’Yan Sandan Metropolitan, Detective Sergeant Claudine Manning, ta ce jami’anta na aiki ba dare ba rana domin gano inda yake tare da kama shi.
“Tawagara ta jami’an bincike na aiki ba tare da gajiyawa ba domin gano inda Temitope Segun yake tare da kama shi.
“Yana da muhimmanci jama’a su tuntubi ’yan sanda ta lambar gaggawa ta 999 idan suka gan shi ko kuma suna da bayanin inda yake,” inji ta.
Rundunar ’Yan Sandan Metropolitan ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma farautar wanda ya tsere daga gidan yari
