‘Yan sandan Katsina sun kama mutane huɗu bisa zargin satar yara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama mutane huɗu cikin su har da masu sanar POS bisa zargin satar ƙananan yara don neman kuɗin fansa tare da ceto yaro ɗan shekara uku.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka ya ce wanda magidanci Abubakar Ahmed Rufa’i ya kai koke ga ‘yan sanda game da sace yaron sa ɗan shekara huɗu da rabi inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan biyar a matsayin kuɗin fansa.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa daga baya ɓarayin sai suka rage kuɗin zuwa dubu ashirin kuɗin abincin da aka ciyar da yaron.

Yace bincike da jami’an ‘yan sanda suka gudanar ya kai su ga kama mutane biyu Abubakar Muntari da Aminu Idris masu sana’ar POS bisa zargin karɓar kuɗin abinci daga mahaifin yaron suka turawa ɓarayin.

Haka kuma a wani lamari irin wannan Malam Abdulrahman Bello shima ya kai rahoto ga ‘yan sanda kan sace yaron sa Yakubu Abdulrahman ɗan shekara uku da haihuwa, inda ɓarayin bayan sun buƙaci biyan kuɗin fansa sun kuma nemi ƙarin Naira 100,000 a matsayin kuɗin da suka ciyar da yaron.

DSP Abubakar Sadiq ya ce bincike da yan sanda suka gudanar ya kai suka ga kama Abdulkarim Mustapha ɗan shekara 16 a wajen masu sanar POS lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗaɗen fansa.

Yace masu sanar POS sun faɗawa ‘yan sanda cewa Abdulkarim Mustapha shine wanda ya karbi kuɗin da ɓarayin suka nema a biya Naira dubu ashirin na abincin yaron Ahmed Abubakar Rufa’i da suka sace tunda farko.

Duk waɗanda ake zargi sun tabbatar da aikata laifin wanda hakan ya taimaka wa yan sanda ceto Yakubu Abdulrahman ɗan shekara uku da haihuwa.

A wani samame da ‘yan sanda suka gudanar sun sami nasarar kama Aminu Musa ɗan shekara 20 da haihuwa wanda ake zargi da faɗawa iyayen waɗanda aka sace abinda za su bada a sako yaran su.

Haka kuma kamar yadda DSP Sadiq yace ‘yan sanda sun kuma gano SIM card da masu garkuwa da mutane ke amfani da su wajan aiki ɓarnar su.

Ɓarayin sun tabbatar wa yan sanda da haɗin kan Ibrahim da Mohammed da aka fi sani da Malam wajan aikata miyagun ayyukan su.

DSP Abubakar Sadiq ya bayana cewa rundunar ‘yan sanda na nan na ƙoƙarin kamo sauran ɓarayin da masu taimaka masu.

By ukarofi

Leave a Reply