‘Yan sandan Kebbi na binciken kisan gillan da aka yi wa ɗalibin jami’a

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi na gudanar da binciken kisan gilla da aka yi ma wani ɗalibi dake matakin karatu aji uku (300 level), da ke jami’ar gwamnatin tarayya Birnin Kebbi, FUBK, Zaharadden Nuhu.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar 11/6/2026, a cikin wani gida mai-zaman-kanshi dake Kalgo, wanda mafi yawan mazauna cikinsa ɗalibai ne, amma ba ɗakunan kwana bane mallakin hukumar jami’ar.

A binciken share fage da ‘yan sanda suka gudanar, an samu mamacin da raunuka, kuma aka garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya, (Federal Teaching Hospital), da ke Birnin Kebbi, amma ‘ajali-yayi-kira’, ya rasu a lokacin da ake masa magani.

Har yanzu dai, ba’a gane waɗanda suka tafka wannan ɗanyen aiki ba.

A wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya bayyana cewar, ana samun labarin afkuwar lamarin, jami’an ‘yan sanda suka dira a gidan, suka killaceshi, domin gudanar da bincike.

“Ba su yi wata-wata ba, suka duƙufa wurin bincike da nufin gano dalilin da ya sanya wani mutum ko wasu mutane, suka aikata wannan abin ash-sha, domin a cafke su”,

“Rundunar na kira ga jama’a, musamman mazauna ƙaramar hukumar Kalgo da kuma ɗalibai, da su kwantar da hankalinsu, su daina zato ko zargi”,

“Wannan mummunar lamari, akwai-ban-takaici, amma ‘yan sanda na bai wa jama’a shawara su guje ma hanzarin ɗora laifi akan wani, domin kaucema tada husuma ko kawo barazana ga wata al’umma ko wani jinsi na mutane”,

“Rundunar ‘yan sandar na bai wa duk wani mai muhimmim bayani dangane da lamarin, ƙwarin-gwiwa, da ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko kuma a buga waya zuwa ofishin ‘yan sanda na ‘kar ta-kwana’ mai lambobin waya, 09039911876 ko 07081074395”,

“Duk bayanan da aka bayar, za’a sirrantasu, sannan kuma a sirranta sunan wanda ya bada rahoton”, Rundunar ta tabbatar.

By ukarofi

Leave a Reply