Yan sandan Zamfara sun ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su, sun kama 10 da ake zargi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce a yau Litinin ta ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su ‘yan asalin kananan hukumomin Bungudu da Maru dake jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba N. Elkanah ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a yau Litinin.

A cewarsa, an sace mutanen ne a watan Maris da farkon watan Afrilu na wannan shekara.

Ya Kara da cewa, waɗanda abin ya shafa sun hada da, maza 8, mata 15 ciki har da uwa mai shayarwa da yara 16 waɗanda aka sace a ƙauyuka da wurare daban-daban a ƙananan hukumomin Bungudu da Maru na jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa tuni jami’an ‘yan sandan haɗin gwiwa da kungiyoyin likitocin gwamnatin jihar suka yi wa waɗanda lamarin ya shafa gwajegwajen da ya dace tare da basu magani.

Da yake karɓar waɗanda abin ya shafa, Sarkin Bungudu Alh. Hassan Attahiru ya godewa rundunar ‘yan sanda bisa yadda suka ceto wadanda lamarin ya shafa ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya bisa ƙoƙarin da ake na magance matsalar rashin tsaro a jihar domin a samu zaman lafiya.

Hakazalika, CP. Ayuba Elkanah ya bayyana cewa rundunar sa ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da ‘yan haramtacciyar ƙungiyar (Yansakai).

A cewarsa, abubuwan da aka samu a gurin waɗanda ake zargin sun haɗa da bindigogi kirar gida, babur 1, motar Honda 2012, babura 4.