Sin ta fitar da tsarin kafa kasuwar cikin gida ta bai ɗaya

Daga CMG HAUSA

Mahukuntan ƙasar Sin sun fitar da tsarin gaggauta kafa kasuwar cikin gida ta bai ɗaya, wadda za ta kasance mai inganci, mai biyayya ga dokoki, da daidaito, kuma bisa tsarin gogayya mai nagarta.

Tsarin wanda kwamitin ƙolin JKS, tare da majalissar gudanarwar ƙasar Sin suka yi haɗin gwiwar fitarwa, na da nufin bunƙasa inganci, da faɗaɗar kasuwar cinikayya ta cikin gidan ƙasar Sin. Ana kuma fatan tsarin zai samar da daidaito, da adalci, da bayyana komai a fili, da damar iya hasashen yanayin hada-hadar cinikayya, da rage kuɗaɗen gudanar da cinikayya.

Ƙari kan hakan, tsarin zai bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙiren kimiyya, da daga matsayin masanaantu, da bullo da sabbin damammaki na shigar masu takarar cinikayya na ƙasa da ƙasa, da hadin gwiwa a kasuwar ƙasar.

Kaza lika, za a ƙara azama wajen inganta tsarin haɗe sassan dokokin mallakar fasaha, da aiwatar da tsarin samar da damar shiga kasuwar bai daya, da ƙara kyautata haɗaɗɗen tsarin samarwa alumma lamuni.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan