Yan takarar PDP a Gombe sun ƙi amincewa da shigar Pantami takara

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE

Wasu daga cikin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe sun bayyana rashin amincewarsu da raɗe-raɗin da ke yawo kan yunƙurin tsohon ɗan takarar gwamna a APC, Farfesa Isa Ali Pantami, na komawa PDP domin neman tikitin gwamna.

A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar ranar Asabar, ‘yan takarar sun ce sun amince da bai wa shugabannin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo damar tantance ɗan takara ɗaya da zai wakilci PDP a zaɓen gwamna mai zuwa.

Sun bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga buƙatar tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma mutunta tsarin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar, inda suka ce sun rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da duk shawarar da shugabannin PDP za su ɗauka.

Sanarwar ta kuma nuna adawarsu da duk wani yunƙuri na bai wa wani ɗan takara damar shiga zaben fidda gwani na PDP bayan ya riga ya shiga irin wannan tsari a jam’iyyar APC a ranar 21 ga Mayu, 2026.

A cewarsu, ɗaukar irin wannan mataki na iya haifar da rikicin siyasa da kuma matsalolin shari’a da za su iya kawo cikas ga jam’iyyar kafin babban zaɓe.

Waɗanda suka sanya hannu a sanarwar sun haɗa da Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki, Usman Aliyu Garry da Monica Kaltho.

By ukarofi