An garƙame Fadar White House yayin da ɗan bindiga suka buɗe wuta a Washington D.C

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar ne wani ɗan bindiga ya buɗe wuta kusa da Fadar White House a yammacin ranar Asabar, inda jami’an tsaron Secret Service na Amurka suka harbe shi har lahira bayan musayar wuta.

Rahotanni sun ce wani mutum da ke wajen shi ma ya samu rauni sakamakon harbin.

A lokacin da lamarin ya faru, Shugaban Amurka Donald Trump yana cikin White House amma bai samu wata illa ba.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa mutumin ya fito da bindiga daga cikin jaka sannan ya fara harbi kusa da shingen tsaron fadar, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa.

Trump ya yaba da matakin gaggawar da jami’an tsaro suka dauka, yayin da kafafen yada labarai suka bayyana wanda ake zargin da suna Nasire Best mai shekaru 21 daga Maryland.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun killace yankin yayin da mutane da ‘yan jarida suka rika gudu domin tsira daga harbe-harben.

By Babaji