2027: PRP ta tantance Donald Duke da wasu biyu don zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar PRP ta tantance tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke da wasu mutum biyu don shiga zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Za a gudanar da zaɓen ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta ce, tantancewar wani ɓangarene na shirye-shiryenta domin tunkarar babban zaɓen 2027.

Sakataren yaɗa labaran PRP na Ƙasa, Muhammad Ishaq ne ya sanar da haka a wata takarda.

Waɗanda aka tantance sun haɗa da Donald Duke, masanin tattali Dakta Nnaoke Ufere da Jihar Abia da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC, Yakubu Mohammed Kingsley daga Jihar Edo.

Ishaq ya bayyana cewa, jam’iyyar ta shirya tsaf wajen ganin ta yi zaɓe mai tsafta tare tabbatar da kiyaye dukkan ƙa’idojin dimukraɗiyya a matakin cikin gida.

A yanzu dai ta ce, aƙalla ‘yan takarar guda 260 ne suke neman kujerun siyasa a ƙarƙashin inuwarta a matakai daban-daban a babban zaɓen da ke tafe.

By Babaji