
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar Abuja ya tafi Cotonou a Jamhuriyar Benin, inda zai halarci taron ƙaddamar da Shugaba Romuald Wadagni na ƙasar.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata takarda, ranar Asabar.
Shettima zai haɗu da shugabannin ƙasashen Afirka a babban taron rantsar da shugaban, wanda za a yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Cotonou a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, 2026.
Nkwocha ya bayyana cewa, Nijeriya da Jamhuriyar Benin sun jima da alaƙar al’ada da tattali da kuma haɗin kai a fannonin tsaro, kasuwanci da makamashi.
A cewar sanarwar, Shettima ya samu rakiyar manyan mataimaka da manyan jami’an gwamnati domin ziyarar aikin.
Ana sa ran zai dawo Nijeriya ne da zarar an kammala taron rantsarwar.
