’Yan wasan Kamaru 32 sun gaza tsallake gwajin shekarun ‘yan ƙasa da 17

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Lokacin na ƙara ƙurewa tawagar Kamaru ta ’yan qasa da shekara 17 domin bayar da sunayen ’yan wasan da za su buga mata wasannin share fage na Gasar Kofin nahiyar Afrika.

Wannan ya biyo bayan matsawar da Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar, Samuel Eto’o ya yi, kan cewa sai an yi wa ko wanne ɗan wasa gwaji, wanda da yawa suka gaza tsallake gwajin.

Tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan ya dage sai an yi amfani da na’urar gwajin shekaru ta (MRI) domin tantance ’yan wasan a filin atisayensu da ke Mbankomo, a wajen birnin Yaounde.

Cikin ’yan wasa 30 na tawagar, 21 sun gaza tsallake gwajin shekarun.

An gano wani koma baya da Kamarun ta ƙara fuskanta shi ne, wasu ’yan wasa 11 na daban su ma sun gaza cin gwajin a ranar Talata, waɗanda a yanzu haka mai horarwa Jean Pierre Fiala ke ta faman yadda zai maye gurbinsu.

Kamaru za ta karɓi baƙuncin Congo da Chadi da DR Congo da Kuma Jamhuriyyar Afrika Ta Tsakiya a wasannin share fagen gasar qungiyoyin Afrika tsakanin 12 zuwa 24 ga watan Janairu.

Inda za a nemi ƙasashe biyu kawai da za su iya kai wa ga gasar Kofin qasashen Afrika na ’yan ƙasa da shekara 17 da za a yi a Algeria.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru cikin wata sanarwa da ta fitar tace, Eto’o ne ya bayar da umarnin a ɗauki wannan mataki domin kaucewa bayar da bayanan karya na shekarun ’yan wasa, wanda ƙasar ta riƙa fama da shi a baya.

“Hukumar Ƙwallon Ƙafar ta shawarci duka masu ruwa da tsaki da su tabbatar da shekaru sun yi daidai domin girmama juna.”