Saudiyya ta halasta wa Ronaldo zaman daduro da farkarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan amsar Cristiano Ronaldo a matsayin sabon ɗan wasan ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, hukumomin ƙasar za su sahale masa cigaba da zaman daduro da budurwarsa, Georgina Rodriguez, duk da cewa, hakan ya saɓa da dokokin ƙasar, waɗanda suka dace ds Shari’ar Musulunci.

Haka nan, hukumar gasar ƙasar ta ƙulla yarjejeniya da tauraron DSTV, don yaɗa wasannin gasar ƙasar a tashar DSTV sakamakon taka leda da Ronaldo zai fara yi a gasar wasannin ƙwallon ƙafa na ƙasar.

Za a riƙa nuna gasar ne a tashar ta talabijin ta DSTV ɗin mai lamba 240. Wato kowa zai iya kallon wasannin Al Nassr a tashar 240 kenan.

Wannan shi ne karo na farko a tarihi da za a nuna gasar wasannin Asiya da Larabawa ta talabijin a tashar DSTV.

A ɗaya ɓangaren kuma, Hukumomin Saudiyya na shirin kau da kai daga dokokin auratayya na ƙasar, domin yarje wa sabon tauraron ɗan wasan da ƙungiyar Al Nassr ta sayo, wato Cristiano Ronaldo, zama da farkarsa Georgina Rodriguez.

Dokokin Saudiyya dai sun haramta mace da miji da ba muharramai ba su yi rayuwa tare ba tare da aure ba.

To, sai dai wata jaridar wasanni na ta ƙasar Spain (SPORTS) ta ruwaito cewa Ronaldo zai yi zaman daduro da Rodriguez a ƙasar Saudiyya kuma da alama ba za a hukunta su ba saboda karya doka.

Ronaldo ya koma Al Nassr ne daga Manchester United bayan da aka soke kwantiraginsa da kulob ɗin sakamakon wata hira da ɗan wasan na Portugal ɗin ya yi a watan Nuwamba da wani mai gabatar da shirye-shirye na Birtaniya, Piers Morgan, wanda ya caccaki club ɗin a ciki.

Ɗan wasan mai shekaru 37 ya yi kakkausar suka ga shugabannin Man United yana mai cewa babu wani ci gaba da ƙungiyar ta samu tun bayan tafiyar Sir Alex Ferguson. Ya kuma caccaki kocin United, Erik ten Hag, yana mai cewa ba ya ganin ƙimarsa.