PDP ta yaba wa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Sakkwato

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke garin Sakkwato ta yanke a ranar Juma’a inda ta tabbatar da Dr. Dauda Lawal Dare a matsayin ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ta PDP a zab’ɓe mai zuwa a jihar.

Shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar, Muktar Lugga ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Gusau ranar Asabar.

A cewarsa, hukuncin da kotun shaida ce ƙarara cewa ɓangaren shari’a shi ne fata na ƙarshe ga duk ‘yan ƙasar nan masu bin doka da oda.

“A gaskiya muna da ƙwarin gwiwar cewa hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Sakkwato ta yanke a baya-bayan nan wanda ya tabbatar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar mu a matsayin ɗan takara, hakan ya nuna cewa ɓangaren shari’a suna matuƙar ƙoƙarin ganin sun ƙwato wa kowa haƙƙinshi, kuma Jam’iyyar PDP a Zamfara na yaba wa kotu kan yadda take tafiyar da shari’a ba son zuciya”.

Idan dai za a iya tunawa wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a garin Gusau na jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Aminu Bappa-Aliyu ta soke Zaɓen fidda gwanin da ta tsayar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, yayin da kotun ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar PDP ba ta da dan takarar gwamna jihar a zaɓen na bana.

Lugga ya bayyana ƙwarin guiwar cewa Jam’iyyar PDP a Zamfara za ta lashe zabe mai zuwa, inda ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da magoya bayan jam’iyyar da su kasance masu bin doka da oda tare da nisantar duk wani nau’i na tada tarzoma a lokacin yaƙin neman zabe da ma bayanta zaɓen domin samun nasarar jam’iyyar.

Ya kuma yi nuni da cewa, jam’iyyar ta tsara dukkan tsare-tsare domin ƙaddamar da yakin neman zaben ta da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Janairun 2023 a jihar.

Ya yi alƙawarin gudanar da yakin neman zaɓe cikin lumana ba tare da wani hargitsi ba a jihar, sannan ya buƙaci ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar PDP da magoya bayan jam’iyyar da su bi duka ƙa’idojin da jam’iyyar ta tanada domin tabbatar da yaƙin neman zaɓe a jihar cikin lumana.