Ɗalibi ya bindige malama a cikin aji a Amurka

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Wani ɗlibi ɗan shekara shida ya buɗe wuta a cikin aji a wata makarantar firamare da ke Jihar Virginia a gabashin Amurka a ranar Juma’a, inda ya yi wa wata malama mummunan rauni.

Sai dai babu ɗalibi ko guda da ya jikkata sakamakon harbin.

“A halin da ake ciki, ɗalibin ya yana hannun ‘yan sanda,” kamar yadda shugaban ‘yan sandan yankin, Steve Drew ya bayyana a wani taron manema labarai.

Ya ƙara da cewa, “wannan ba harbin ganganci ba ne.”

‘Yan sanda sun ce wanda aka harba ɗin malama ce a makarantar kuma ana kyautata zaton raunin da ta samu yana da haɗari ga rayuwa.

“Ina cikin kaɗuwa, kuma na karaya,” in ji shugaban makarantun birnin, George Parker.

Ya ce, “Muna buƙatar goyon bayan al’umma don tabbatar da matasa ba sa ta’ammali da bindigogi.”

Rikicin makaranta ya addabi Amurka, inda aka fuskanci bala’o’i na baya-bayan nan ciki har da kisan yara 19 da malamai biyu a watan Mayun da ya gabata a Uvalde, Texas, da wani ɗan bindiga mai shekaru 18 ya yi.

Kazalika, an yi ƙiyasin mutuwar mutane 44,000 masu nasaba da harbin bindiga a Amurka a shekarar da ta gabata, kusan rabinsu sun haɗa da kashe-kashe, haɗurra da kare-kai, sannan wasunsu sun kashe kansu, kamar yadda PRNigeria ta rawaito Cibiyar Ƙididdigar Rikice-rikice Masu Nasaba da Bindigogi.