Rasha ta dawo da ruwan wuta kan Yukiren

Daga AMINA YUSUF ALI

Bayan sanarwar da ta yi na a tsagaita wutar yaƙi tsakaninta da Yukiren na tsawon awoyi 36 saboda murnar Kirismeti, a yanzu haka ƙasar Rasha ta yi amanta ta lashe ta karya tsagaita wutar.

A yanzu dai Shuagaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha ya ci gaba da luguden wuta na ababen fashewa ga abokiyar karawar tasu, Yukiren.

Da ma tuntuni Putin ya yi umarni ga ministansa na tsaro, Sergei Shoigu, da ya bayar da sanarwar tsagaita wuta na tsawon awoyi 36 daga 6 ga watan Janairu zuwa tsakiyar dare na 7 ga watan.

Sai dai bayan awoyi ƙalilan da ba da sanarwar tsagaita wutar, Rasha ta ci gaba da ɓarin wuta a wani gari dake gabacin ƙasar Yukiren, wai shi Bakhmut. Kamar dai yadda Kyrylo Tymoshenko, mataimakin shugaban ofishin shugaban ƙasar Yukiren ya bayyana.

Inda ya ƙara da cewa, varin wutar da Rashan ta yi ba Bakhmut kaɗai ya shafa ba, har da birnin Kramatorsk.

A cewar Kyrylo, mayaƙan Rasha sun harba roka har sau biyu a birnin Kramatorsk. “Kuma a haka wai suke maganar tsagaita wuta”. Inji shi.

A cewar sa, rokokin da aka harba sun tashi da gidajen al’umma har guda 14 a birnin Kramatorsk.

Sai dai a cewarsa, ba a samu kisa ko jikkatar ko mutum guda ba.

Hakazalika, ya ce jim kaɗan bayan sanarwar tsagaita wutar, a yankin Kherson na Yukiren ma Rasha ta ɗana ababen fashewa a hukumar kashe gobarar Yukiren da wasu gine-gine da suke maƙwabtaka da ita. Kuma an samu mutuwar mutum guda, da jikkatar mutane da dama.

Kodayake, da ma su Yukiren sun ɗan yi shakku bisa wannan Hutu na tsagaita wuta da Rasha ta ba da sanarwar. Domin sun zargi cewa, wannan hutun da Rashan ta ce a tafi wataƙila wata dabara ce da ta yi ta shagaltar da abokan gaba da zai sa ta ƙara shiri mai kyau. Shi ya sa tun a gurbi, Yukiren ɗin ta nuna ba ta son wannan hutun. Sai suka kasance cikin shirin su.

Sai dai kuma ma’aikatar tsaron ƙasar Rasha ta bayyana cewa, da ma ƙasar Rasha ta fara hutun tsagaita wutar kenan, sai kuma a cewar sa suka zargi Yukiren da jefa ababen fashewa a taron al’umma da kuma maɓoyun sojoji. Shi ne su ma suka ɗauki mataki.

Shi dai wannnan burin da Rasha ta bayar ya yi dai-dai da hutun bikin Kirismeti da ta saba bayarwa kowacce shekara a ranar 7 ga Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *