Mulkin soji ya fi na Buhari kyautawa – ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya ASUU, ta ce mulkin soji ya fi na gwamnatin farar hula, musamman wajen kyautata jin daɗin malamai a Nijeriya.

Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke shi ne ya bayyana hakan ranar Talata 5 ga Janairu, 2023, a wajen wani taron ƙaddamar da wasu littafan karatu guda 50 na manyan makarantu da marubutan Nijeriya suka wallafa ƙarƙashin tallafawar Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na Nijeriya (TETfund), a Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’a ne 16 ga Oktoba, 2022 ASUU ta janye yajin aikin watanni takwas da ta kwashe tana yi ba tare da an gudanar da harkokin karatu a jami’o’in gwamnatin ƙasar ba bisa neman sai Gwamnatin Tarayya ta cika dukkan alƙawurran da ta ɗauka musu a shekarun baya.

Haka zalika, bayan janyewar yajin aikin sai kuma wasu batutuwa suka bijiro a ranar Alhamis, 3 ga Nuwamba, 2022 inda Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’ar rabin albashi na watan da suka koma kan aiki.

Sai dai kuma, daga baya Ministan Ilimi na Nijeriya ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta biya malaman akan aikin da ba su yi shi ba, inda gwamnati ta fito ta tsarin “ba aiki ba biya.”

Matsayar da gwamnati ta ɗauka na riƙe albashin malaman ya haifar da ce-ce-ku-ce iri-iri a faɗin ƙasar da kuma wasu rassa na jami’o’in ƙasar, inda suka dinga kiraye-kirayen da a sallami Ministan Ilimi Adamu Adamu da kuma Ministan Qwadago, Dr. Chris Ngige daga aikinsu.

Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, Osodeke ya ce: “Ina gode wa Minista da kuma duk mutanen da suka zo nan wajen yau. Ina son in yi wa ‘yan uwana godiya akan tado da wannan batu wanda kuma nake ganin yana da muhimmanci qwarai da gaske. Ina so in ɗan faɗi abu kaxan dangane da TETfund da kuma yadda ta samo asali.

“Na ga cewa zamanin mulkin soja malaman jami’a sun fi jin daɗi da walwalar gudanar da aikinsu,” inji Osodeke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *