Kotu ta tabbatar da zaɓen fid-da gwanin PDP na takarar gwamnan Zamfara

Daga WAKILINMU

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Sakkwato ta tabbatar da Dr Dauda Lawal-Dare a matsayin ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara a zaɓen 2023.

A ranar Juma’a Kotun ta soke hukuncin da a baya ya soke takarar Dauda Lawal Dare wanda PDP ta gabatar a matsayin ɗan takarar gwamnan Zamfara a zaɓe mai zuwa.

Wannan na zuwa ne bayan da farko Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, ta soke zaɓen ɗan takarar Gwamna Jihar Zamfara da PDP ta gudanar, wanda Dauda Lawal ya lashe.

Rikicin zaɓen tsayar da ɗan takarar Gwamnan Zamfara a PDP dai ya fara kai masu neman takarar zuwa kotu, inda ta soke zaɓen ta sa a gudanar da sabo.

A zaben fid-da-gwanin da PDP ta gudanar ranar 25 ga watan Mayu, 2022, Dauda Lawal ya samu ƙuri’a 431, wanda ya ba shi damar zama ɗan takarar gwamnan Zamfara a inuwar jam’iyyar.

Tun farko, ’yan takara uku a zaɓen; Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki da kuma Ibrahim Shehu-Gusau, sun janye daga zaɓen saboda abin da suka kira da rashin bin ƙa’ida.

Amma a lokacin, baturen zaɓen, Adamu Maina, ya ce janyewar tasu haramtacciya ce, saboda ba su sanar a hukumance ba.

Daga bisani a watan Yuni, Shehu-Gusau, Madawaki da kuma Aliyu Hafiz Muhammad — shi ma mai neman takara — suka garzaya kotu suna neman a soke zaɓen da Dauda Lawal ya lashe a matsayin ɗan takarar Gwamnan Zamfara a PDP, saboda abin da suka kira saɓa kundin tsarin jam’iyyar.

A watatn Satumba ne Mai Shari’a Aminu Bappa ya amsa roƙonsu tare da soke zaɓen fid-da-gwanin da Lawal Dare ya lashe, sannan ya ba da umarnin a gudanar da sabo.

Sai dai daga bisani, alƙalin a wani zama na daban ya soke zaɓen ɗan takarar da PDP ta gudanar tare da haramta mata tsayar da ɗan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a zaɓen 2023.

Sai a Juma’ar da ta gabata Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Sakkwato ta soke hukuncin Babbar Kotun.