Ƙananan hukumomin Borno 2 na hannun Boko Haram – Zulum

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya tabbatar cewa a halin da ake ciki Boko Haram na riƙe da wasu ƙananan hukumomi biyu a jihar.

Ya ce ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa su ne; Guzamala da Kukawa da ke yankin Borno ta Arewa.

Zulum ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a.

Yayin ziyarar tasa, Zulum ya shaida wa manema labarai cewa hakan ba zai hana shi gudanar da zaɓe a yankunan da lamarin ya shafa ba.

“Insha Allah, ba mu da kowace matsala a Jihar in Borno,” in ji Gwamnan.

Ya ƙara da cewa, “An samu ci gaba da kashi sama da 90 a fannin tsaron jihar, don haka ba mu da matsala. Jama’a za su iya zuwa kaɗa ƙuri’a ranar zaɓe.”

Ya ce an samu cigaba mai ma’ana a sha’anin tsaron jihar idan aka kwatanta lamarin tsaro a 2015 da kuma 2019.

Don haka ya buƙaci jama’a kowa ya tafi gundumarsu don ya karɓi Katin Zaɓen da za su yi amfani da shi a zaɓe mai zuwa.

Haka nan, ya ce aikin gyare-gyare na kan gudana, kuma nan ba da daɗewa ba za a maido da ‘yan gudun hijirar jihar da ke Nijar da Kamaru gida.