Rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani a Ondo

*An rasa ran mutum
*Gwamnatin jihar ta saka dokar ta-ɓaci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mutum ɗaya ya rasa ransa tare da lalata kadarori da dama sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin wasu Fulani da Hausawa mazauna yankin Ogbese da ke Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.

An tattaro cewa, rikicin da ya faro tun a yammacin ranar Talata 3 ga watan Junairun 2022 inda ya yi ƙamari da safiyar Laraba 4 ga watan Junairun 2022, wanda aka qona shaguna da dama na ’yan Arewa a babbar kasuwar garin.

Har yanzu dai ba a san ainihin musabbabin faɗan a hukumance ba har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, amma an gano cewa tashin hankali ya mamaye yankin.

Sai dai wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, rikicin ya samo asali ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin wani Bafulatani da ke zaune a dajin da kuma wani Bahaushe a cikin yankin kan zargin tabar wiwi da aka fi sani da Indiya.

Ya bayyana cewa, ana zargin Bafulatanin ya saci fakitin tabar wiwi da Bahaushen ya ajiye a daji.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Su biyun sun fafata ne a kan wani fakitin wiwi da Bahaushen ya ajiye a cikin daji. A ranar Talata ne faɗan ya kai yankin baki ɗaya. Ya faru ne bayan kashe ɗaya daga cikin Bafulatani a rikicin, sannan aka aona shaguna na Hausawa cikin dare. Amma tun ranar Talata muna ganin ’yan sanda da wasu jami’an tsaro suna sintiri a garin.

A martanin da ta mayar, Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’yan Sandan jihar (PPRO), Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da cewa an ƙona shaguna takwas a rahoton da ta samu amma ta musanta rahoton rikicin.

“Babu wani rikici tsakanin Hausawa da Fulani a Ogbese, ’yan sanda sun samu rahoton cewa kimanin shaguna takwas ne suka ƙone ƙurmus da tsakar dare,” inji PPRO.

A wani labarin kuma, Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya ƙaƙaba dokar zaman gida ta tsawon awanni 24 a kowace rana a garin Ikare-Akoko, hedkwatar Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa maso Gabas.

Rahotanni sun nuna cewa, gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan danvarwan da ta ɓarke har da kashe-kashe a wurin shagalin shigowar sabuwar shekara.

An ce rashin zaman lafiya ya mamaye garin ne ranar Talata lokacin da shagalin sabuwar shekara da matasa suka shirya ya sauya salo, aka fara ruwan harsashi.

Rahotanni daga garin Ikare sun nuna cewa masu ba da nishaɗi a wurin da mazauna yankin sun ari na kare domin tsira da rayuwarsu.

A cewar wasu majiyoyi, harin ‘yan bindigan da ya wargaza shagalin ba zai rasa alaƙa da faɗan ƙarfin iko tsakanin basaraken Owa-Ale da kuma Olukare na Ikare, Sarakuna biyu da ake da su a garin.

Ƙaƙaba dokar zaman gidan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a Akure ɗauke da sa hannun Sakataren Watsa Labaran Gwamna, Richard Olatunde.

Sanarwan ta ce, an ɗauki matakin sanya dokar ne a wurin taron tsaro na jihar Ondo ƙarƙashin shugabancin mai girma gwamna.

Wani sashin sanarwan ya ce, “An yi haka ne bayan ƙara tsanantar rikici wanda ya samo asali tun ranar Talata, ya ci gaba da yaɗuwa ba tare da kawo ƙarshensa ba kuma gwamnati ta zauna a manyan Sarakuna da nufin shawo kan mutane.”

“Muna umartan jami’an tsaro su tabbatar mutane sun bi wannan doka sau da kafa, tuni aka ƙaddamar da bincike domin zaƙulo asalin abinda ya haddasa rikicin.”

“Domin dawo da zaman lafiya, gwamnati ta garƙame Ikare-Akoko bakiɗaya, ba a son ganin motsin kowa a waje ba tare da izinin mahukunta ba har sai ‘baba ta gani’.