Da Ɗumi-ɗumi: NRC ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Sufurin Jirgin Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta rufe tashar jirgi da ke Ekehen a Jihar Edo har sai ‘baba ta gani’.

Hukumar ta ba da sanarwar rufe tashar ne a zaurenta na WhatsApp inda takan yi mu’amala da fasinjoji.

Sanarwar ta ce, “Ana sanar da ɗaukacin jama’a musamman fasinjojinmu cewa, mun rufe tashar Ekehen na wucin-gadi saboda matsalar tsaro.”

Kazalika, wata sanarwa ta ce, “Saboda halin da tashar Ekehen ta faɗa ranar Asabar, jirgi mai lamba WITS 01/ 02 ba zai sake tsayawa ba a Tashar Ekehen.”