NANS ta nemi agajin Buhari don hana ƙarin kuɗin makaranta

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS) ta nuna rashin yardarta kan take-taken Gwamnati na neman ƙara kuɗin makaranta na jami’o’in tarayya da kashi 200 daga wannan shekara.

Wannan ya sa ƙungiyar ta ce tana kira da babbar murya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taimaka ya gaggauta sa baki don taka wa shirin burki kafin hakan ya ta da ƙura a ƙasa.

Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta ne cikin wasiƙar da ta aike wa Shugaba Buhari mai ɗauke da kwanan wata 4 ga Janairu, 2023.

Wasiƙar ta samu sa hannun Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Usman Umar Barambu da kuma Shugaban majalisar dattawanta, Attah Unalue Felix.

Ministan Ilimi, Sakataren Hukunar Kula da Jami’o’i (NUC), Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai da sauransu, na daga cikin waɗanda ƙungiyar ta aika wa da kwafin wasiƙar.

NANS ƙungiya ce da ta tattara ɗaliban Nijeriya na marakarantun gaba da sakandare a gida da waje wanda a halin yanzu take da mambobi kimanin miliyan 50 a faɗin duniya.