Buhari zai wadata Burundi da fetur duk da ƙarancinsa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya za ta wadata ƙasar Burundi da man fetur, inda ya yi alƙawarin cewa Kamfanin Man Fetur na Nijeriya zai duba buƙatar ƙasar na tallafin makamashi.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa ranar Talata yayin da yake karɓar baƙoncin Shugaba Ƙasar Burundi, Evariste Ndayishimiye, wanda yazo da buƙatar.

“A kan neman taimako a fannin samar da makamashi musamman man fetur da shugaban ƙasar Burundi ya yi, shugaba Buhari ya ce, ya san yadda ƙasar ke fama da ƙarancin makamashi, kuma ya yi alqawarin cewa zai saka kamfanin man fetur na Nijeriya duba buƙatar.

“A cikin ruhin haɗin kai da ’yan uwantaka na Afirka, Nijeriya za ta tallafa wa Jamhuriyar Burundi ta hanyoyi daban-daban kamar yadda ya kamata,” inji shi.

Alƙawarin da Buhari ya yi na tallafa wa Burundi da samar da mai ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya suka fara samun fetur ɗin da za su saya bayan da aka daɗe ana fama da ƙarancin mai a ƙasar.